Barazanar sanya takunkumi a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 19.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barazanar sanya takunkumi a Sudan ta Kudu

Amirka da EU su bukaci shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar da su mutunta yarjejeniyar da ke tsakaninsu idan suna son kansu da lafiya.

Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Amirka sun yi barazanar kakaba wa 'yan tawayen Sudan ta Kudu da kuma gwamnatin wannan kasa jerin takunkumai, idan suka ki sulhunta rikicin da ke tsakaninsu tare da mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma. Wakilan EU da kuma fadar mulki ta Washington ne suka yi wannan bayani a Addis Ababa gabanin zaman tattaunawa tsakanin bangarori biyu na Sudan ta Kudu da ke gaba da juna.

Tun dai watanni ukun da suka gabata ne dakarun shugaba Salva Kiir da kuma na 'yan tawayen da tsohon mataimakinsa Riek Machar ke shugabanta suke bai wa hamata iska da nufin kankane madafun iko. Lamarin da ya haddasa mutuwar daruruwan 'yan Sudan ta Kudu da ba su ji ba kuma ba su gani ba, yayin da wasu dubbani kuma suka kaurace wa matsugunansu.

A ranar Alhamis ne dai bangaren shugaba Kiir da kuma na shugaban 'yan tawaye Machar za su koma kan teburin tattauna a babban birnin Habasha bisa jagorancin kungiyar raya kasa ta yankin gabashin Afirka wato IGAD.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal