1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam ya halaka rayuka a Najeriya

January 7, 2020

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da wani harin bom da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkatar wasu a tsakanin kasar da Kamaru.

https://p.dw.com/p/3Vo14
Doppelanschlag in Tschad
Hoto: Reuters/M. Ngarmbassa

Akalla mutum 30 ne suka mutu yayin da wasu suka jikkata, sakamakon tashin da wani bom ya yi a wani bangare na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyar.

Shaidu sun ce lamarin wanda ya faru a kan wata kasuwa mai cunkoson jama'a a garin Gamboru, ya ma shafi wani bangare na garin Fotokol na Jamhuriyar Kamaru da ke iyaka da Najeriya.

Sabbin alkaluma na cewa mutum 35 ne suka jikkata a tashin bom din hadin gida da ya auku da la'asariyar jiya Litinin.

Wasu jami'an sa kai sun tabbatar da tashin bom din, duk da cewar hukumomi ba su shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters ba da yammacin na Litinin.

Kungiyar Boko Haram mai gwagwarmaya da makamai dai ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare a jihar Borno da Yobe da kuma jihar Adamawa a Najeriyar.