Bakin haure daga Jamus sun isa Afganistan | Labarai | DW | 07.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure daga Jamus sun isa Afganistan

Jirgin sama dauke da masu neman mafakar siyasa da suka gaza cika sharuda daga Jamus ya sauka a birnin Kabul na kasar Afganistan kamar yadda hukumar da ke lura da bakin haure ta bayyana a wannan rana ta Alhamis.

Jirgin dai dauke da mutane 27 daga birnin Frankfurt ya sauka a kasar ta Afganistan da wadannan mutane kamar yadda kamfanin dillancin labaran Jamus na dpa ya bayyana.

A cewar ma'aikatar harkokin cikin gidan Jamus mutane 17 daga cikin wannan adadi sun kasance masu aikata manyan laifuka. Sannan akwai wasu takwas wadanda suka ki bada hadin kai ga jami'ai wajen bada hakikanin bayanai na kansu. Akwai kuma wasu guda biyu da ke zama masu iya aikata laifi ko da yaushe.

'Yan sanda a kasar ta Afganistan dai sun bayyana cewa babu daya daga cikin mutanen da aka mika a hannunsu a lokacin da suke isa kasar. Tun dai daga watan Disambar 2016 Jamus ta mayar da baki 'yan Afganistan 128 a cikin rukunai bakwai, cikin wannan adadi ban da wadanda aka kai a wannan mako.