Baje kolin litattafai mafi girma a duniya a Jamus | Labarai | DW | 09.10.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baje kolin litattafai mafi girma a duniya a Jamus

An bude bikin baje koli na masana'antun buga litattafai mafi girma a duniya a wannan Talata a birnin Frankfurt na nan Jamus inda ake sa rai kimanin masu baje koli 7,000 za su halarta daga kasashe 110.

Heinrich Riethmueller, shugaban kungiyar masu buga litattafai da masana'antunsu a Jamus ya ce babban burinsu dai shi ne a jawo hankalin al'ummar duniya kan dabi'ar karance-karance da ke samun koma baya.

Wadanda suka shirya wannan bikin bajekoli sun bayyana cewa a bana an samu kari na mahalarta baje kolin litattafan da kashi uku bisa dari idan aka kwatanta da shekarar 2017. An ma a Jamus ciniki na litattafai ya ragu a bana da kashi 1.1 cikin dari.