1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baerbock: Jamus na muradin sasanta rikicin Sudan

Zainab Mohammed Abubakar
January 24, 2024

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta fara wata ziyarar aiki a gabashin Afirka, inda ake saran za ta matsa kaimi kan sanya takunkumi da samar da zaman lafiya a Sudan.

https://p.dw.com/p/4bcuC
Annalena BaerbockHoto: Thomas Imo/photothek/IMAGO

Ku san shekara guda kenan ake gwabza yaki a Sudan tsakanin sojojin da ke biyayya ga babban hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan da na bangaren tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, rikicin da ya kashe mutane sama da 13,000 tare da raba miliyan 7.5 da muhallansu.

Ziyarar ta Baerbock na kwanaki da dama, za ta kai ta Sudan ta Kudu, Kenya da Djibouti, inda ake saran za ta tattauna hanyoyin kare jiragen jigilar kayayyaki a tekun Bahar-Maliya daga hare-haren 'yan tawayen Houthi na Yemen.

Ministar harkokin wajen ta Jamus ta ce tare da takwarorinta na Djibouti da Kenya da Sudan ta Kudu, za su lalubi hanyoyin da za a iya kawo Janar Burhan da Hemeti a kan teburin tattaunawa.