MDD ta ce an halaka mutane dubu goma sha biyar a Sudan
January 23, 2024Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani rahotonta ya gano cewa an halaka mutane dubu goma zuwa dubu goma sha biyar a garin El Geneina kadai na yankin Darfur da ke kasar Sudan, tun bayan barkewar rikici tsakanin dakarun sojin kasar karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan, da na RSF da ke karkashin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo.
Karin bayani:Sudan ta fice daga kasashe membobin kungiyar Igad
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito Majalisar Dinkin Duniyar na kokawa da irin munin take hakkin bil'adama a kasar, tun bayan fara yakin a cikin watan Afrilun bara, tare da raba miliyoyin mutane da gidajensu.
karin bayani:Fatan tattaunawa don kawo karshen rikicin Sudan
Rahoton ya nuna cewa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na nazartar batun, tare da duba yiwuwar kakabawa Sudan din takunkumi a kan cin zarafin 'dan adam, da suka hada da fyade da muzgunawa iri-iri.