Badakalar shari′ar makamai ya ta′azzara rikicin PDP | Siyasa | DW | 19.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Badakalar shari'ar makamai ya ta'azzara rikicin PDP

Wasu mataimakan shugabannin PDP a Najeriya guda hudu sun nemi tabbatar da saukar masu shugabanninsu da ke fuskantar shariár badakala ta makamai

Can a gefe daya dai Kakakin jamíyyar PDP na kasa Oliseh Metuh ya isa harabar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja da ranar wannan Talatar a cikin sarka da farin gemun da ke zaman a sabunba, a yayin kuma da a cikin gidan wadatar da ya dade yana jan zare ana amsawa, kai ke rabe zuwa gida biyu, a wani abun da ke zaman alamu na kara lalacewar lamura a cikin PDP ta adawa.

Wata tuhumar hukumar yakar hancin Tarrayar Najeriya ta EFCC kan kakakin da ma shugaban kwamitin amintattun jamíyyar dai yanzu haka na neman taázzarar lamura gidan na wadata da har yanzu ya kasa zama da nufin tunkarar jan aiki na adawar dake gabansa cikin kasar a halin yanzu.

Babu dai zato ba kuma tsamanni wasu yan kwamitin zartarwar jamíyyar suka nemi ajiye aikin jamián guda biyu da aka ambato a cikin badakalar makaman dake ruruwu irin ta wutar daji yanzu haka. Sannan da komawar shugaban na riko zuwa matsayin mataimakin shugaban jamíyyar da nufin kyale yankin na arewa maso gabas samar da shugabancin da ya dace.

Wata sanarwar da ke dauke da sa hannun mataimakin kakakin jamíyyar na kasa Barrister Abdullahi Jalo, da kuma mataimakin mashawarcin jamíyyar kan harkar shariá Bashir Maidugua kuma mataimakin sakatare na tsare-tsaren jamíyyar Okey Nnaedozei, sannan da mataimakin shugaban matasan PDP Dennis Alonge-niyi, suka nemi jamián ajiya mukaman nasu har ya zuwa lokacin da zaá kamalla shariár da ke daukar hankali ciki dama wajen kasar.

Ana dai kallon sanarwar da ta kai ga tada hankula cikin gidan na wadata, a matsayin wani kokarin juyin mulkin mataimaka na shugabannin jamíyyar da suka share tsawon lokaci suna zaman yan kallo a cikin lamuran PDP.

Sauti da bidiyo akan labarin