Babban taron kungiyar Taraiyar Afrika a Sudan | Labarai | DW | 23.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban taron kungiyar Taraiyar Afrika a Sudan

A yau ne shugabannin kungiyar taraiyar kasashen Afrika zasu zabi sabon shugaba wajen babban taronsu na yau a kasar Sudan.

Sudan kanta tana neman shugabancin kungiyar,sai dai ta samu adawa daga membobi wadanda suke ganin karbar shugabancin zai kawo cikas ga tattaunawar zaman lafiya na darfur,ya kuma bata sunan kungiyar.

Sudan ta nemi shugabancin kungiyar mai membobi 53,bisa aladar cewa dukkan kasa da karbi bakuncin babban taron kungiyar itake zamowa shugabar kungiyar ta gaba,inda a wannan karo sudan zata karbi ragamar kungiyar daga hannun Najeriya idan ta samu nasarar yin hakan.