1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban Taron ƙasa na Jamíyar FDP a birnin Cologne

April 24, 2010

Bayan shekaru goma sha ɗaya tana adawa, a ƙarshe Jamíyar FDP ta sami shiga cikin ƙawancen Jamíyun gwamnatin dake mulki a Jamus.

https://p.dw.com/p/N5Nm
Wakilai a babban taron ƙasa na Jamíyar FDPHoto: AP

A ranar Asabar ɗin nan ce Jamíyar FDP a nan Jamus ta fara babban taronta na ƙasa na kwanaki biyu a birnin Cologne, a karon farko tun bayan nasarar da ta samu a zaɓen gama gari da ya gudana a shekarar 2009 wanda ya bata damar shiga ƙawancen gwamnati da Jamíyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel. Muhimman alámuran da suka fi ɗaukar hankali a taron sune batun manufofin haraji dana lafiya. Bugu da ƙari  da nazari kan manufofin gwamnatin Jamus kan dangantaka da ƙasashen ƙetare da kuma taimakon raya ƙasashe.

Wannan taro dai ya zo ne makonni biyu gabanin zaɓen gundumomi da zaá gudanar a ranar 9 ga watan Mayu mai kamawa inda alúmar birnin na Cologne miliyan 18 kuma birni mafi girma a jihar North Rhine-Westphalia za su kaɗa ƙuriársu. Jamíyar ta FDP ta yi amfani da wannan dama wajen ƙara baiyanawa jamaá manufofinta da kuma inda aka sa gaba.

Shekaru ɗai ɗai har goma sha ɗaya Jamíyar ta kwashe tana adawa, sai dai a ƙarshe kwalliya ta biya kuɗin sabulu domin a shekarar 2009 ta taka rawar gani a zaɓe wanda hakan ya bata damar kasancewa abokiyar ƙawance a gwamnatin haɗaka da Jamíyun CDU da CSU inda kuma ta sami muƙaman Ministoci guda biyar a cikin gwamnatin waɗanda suka haɗa da muƙamin Ministan harkokin waje dana raya ƙasashe dana tattali arziki dana lafiya da kuma maáikatar shariá. Muƙami mafi girma shine na maáikatar harkokin waje wanda aka baiwa shugaban Jamíyar Guido Westerwell.

Sai dai kuma a wani abu da ya saɓa aláda, a duk lokacin da zai yi wata tafiya Westerwelle ya kan sanya abokin zamansa cikin ayarin jamiái yan rakiya abin kuma da ya haifar da cece-kuce a cikin gida. Wannan zargin cewa shugaban Jamíyar ta FDP na zaɓar wanda ya ga dama a cikin yan tawagarsa ya haifar da muhawara mai zafi abin da kuma ya harzuƙa Westerwelle ya maida martani yana mai cewa "Ba zan karaya ba da wannan sukar lamiri, na yi muku alƙawari ko kaɗan wannan ba zai sanya gwiwata ta yi sanyi ba".

Flash-Galerie Guido Westerwelle FDP
Shugaban Jamíyar FDP Guido WesterwelleHoto: AP

Manufar ƙetare na Westerwlle ita ce ɗorawa akan matsayin da ake kai. Ana iya ganin haka ta fannin ayyukan soji da taimakon jin ƙai da Jamus ke bayarwa a Afghanistan wanda Jamíyar FDP ta bada goyon bayanta akan su. Wannan kuwa ya ƙunshi aikin samar da tsaro zuwa shekara ta 2014 inda a wannan lokaci ake fatan jamián tsaron Afghanistan zasu sami ƙwarewar da zasu iya karɓar ragamar tsaron ƙasarsu. Akan wannan matsayi a wani lokaci a cikin watan fabrairu Westerwelle ya yi jawabi da cewa " Wannan tafarki ne managarci da muke ƙoƙarin ganin tabbatuwarsa, to amma ba wai takamammen waádi bane na janyewa, domin ambatar sanya waádi tamkar bada goyon baya ne ga yan taádda wanda kuma wannan kuskure ne".

Haka zalika a lokacin wata ziyarar Afirka da Westerwelle ya kai tare da Ministan taimakon raya ƙasashe Dirk Niebel. Ko da a makon da ya gabata sai da Dirk Niebel ya kare batun ayyukan sojin na Jamus a Afghanistan a wata hira da aka yi da shi a tashar Talabijin dangane da mutuwar wasu sojojin Jamus a ƙasar ta Afghanistan.

A game kuwa da manufar FDP dangane da haraji batun da zasu tattauna a taron na birnin Cologne. Haɗakar Jamíyun ƙawancen CDU da CSU sun amince da shirin harajin ga alúma da harkokin tattalin arziki har ya zuwa shekara ta 2013 kamar yadda Sakataren Jamiyar FDP na ƙasa Christian Lindner yayi bayani. " Zuwa shekara ta 2013 bisa dukkan ƙiyasi abin da ke shigowa aljihun gwamnati zai ƙaru da kimanin kashi 30 cikin ɗari, wanda wannan ke nuni da cewa gwamnati na da hanyoyin sarrafa alámura da dama amma ƙananan hukumomi da kuma ɗaiɗaikun jamaá basu da wannan dama a saboda haka muke buƙatar samun daidaito".

Wani batu mai ɗaukar hankali a taron shine haƙƙin da jamaá ke da shi. Misali Jamíyar ta FDP na da raáyin kare haƙƙin maáikata. A matakin tarayyar turai dai an baiwa batun yaƙi da ayyukan taáddanci babban muhimmanci, to amma ga`yan Jamíyar ta Liberal masu sassaucin raáyi zasu amince ne kawai da naurar binciken surar jikin mutum a filayen jiragen sama idan aka tabbatar da cewa basu da haɗari ga lafiyar fasinjoji sannan kuma aka bada dama na raɗin kai ga wanda ya yi raáyi amma ba wai a tilasta cewa ya zama wajibi ba.

Mawallafa : Marcel Fürstenau / Abdullahi Tanko Bala

 Edita       : Zainab Mohammed Abubakar