Ba za a kada sabuwar kuri′a kan yarjejeniyar Brexit a wannan Litinin ba | Labarai | DW | 21.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba za a kada sabuwar kuri'a kan yarjejeniyar Brexit a wannan Litinin ba

Da a ranar Asabar ya kamata majalisar dokokin Biratniya ta kada kuri'a kan yarjejeniyar Brexit, amma sai aka kada kuri'ar jinkirta amincewa da yarjejeniyar domin hana shiga rudu a kan batun na Brexit.

Firaministan Birtaniya Boris Jonshon ya sake fuskantar koma baya a majalisar dokokin Birtaniya, inda kakakin majalisar John Bercow ya ki amincewa majalisa ta kada kuri'a kan sabuwar yarjejeniyar ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai EU.

Kakakin ya ce dalilin wannan mataki da ya dauka shi ne babu canji a cikin daftarin da wanda gwamnati ta gabatar a ranar Asabar.

Ya ce: "A takaice kudurin na yau daidai yake da na ranar Asabar wanda kuma tuni majalisa ta yanke hukunci a kai. Hakazalika halin da ake ciki bai canja ba. Saboda haka na yanke hukuncin cewa ba za a yi mahawara kan kudurin a yau ba."

Da a ranar Asabar ya kamata majalisar dokokin ta kada kuri'a kan yarjejeniyar ta Brexit a wani zama na musamman da ta yi, amma sai suka kada kuri'ar jinkirta amincewa da yarjejeniyar domin hana shiga rudu a kan batun na Brexit.