B Haram ta fitar da bidiyon ma′aikatan mai | Labarai | DW | 29.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

B Haram ta fitar da bidiyon ma'aikatan mai

Kungiyar Boko Haram bangaren Al-Barnawi ta saki wani bidiyo na wasu mutane uku da ta kama a lokacin kazamin harin da ta kai a ranar Talatar da ta gabata kan ayarin wasu ma'aikatan kamfanin mai na Najeriya na NNPC.


Bangaren Boko Haram na Abu Mosab Al-Barnawi kazalika ta nuna wasu jami'an jami'ar Maidugurida ta capke lokacin wani hari wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 50. 

A cikin bidiyon mai tsawan mintuna hudu, mutanen da suka bayyana kansu a matsayin ma'aikatan jami'ar Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, suna masu kira ga gwamnati da ta biya bukatun kungiyar domin tsira da rayukansu. 

Tuni dai kakakin jami'ar ta Maiduguri Danjuma Gambo ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da cewa ma'aikatansu ne, amma kuma ya ce akwai sauran mutanen da ba su bayyana ba daga cikin jerin ma'aikatan nasu da ke cikin ayarin mutanen da mayakan kungiyar ta Boko Haram ta kai wa hari.