Austriya za ta gina katanga a kan iyakarta da Sloveniya | Labarai | DW | 28.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Austriya za ta gina katanga a kan iyakarta da Sloveniya

Za a karfafa bincike kan iyakokin Austriya da Sloveniya saboda kwararar 'yan gudun hijira da ke bi ta kasashen yankin Balkan suna shigowa Austriya da Jamus.

Österreich Spielfeld Grenze Slowenien Flüchtlinge Zaun

'Yan gudun hijira a bangaren iyakar Sloveniya da Austriya

Ganin yadda matsalar kwararar 'yan gudun hijira ta ki ci ta ki cinyewa, kafofin yada labarun kasar Austriya sun rawaito ministar cikin gidan kasar Johanna Mikl-Leitner na ba da sanarwar cewa kasarta za ta gina wata katanga a kan iyakarta da kasar Sloveniya. Sai dai ministar ta ce manufa ba ita ce garkame kan iyakokin baki daya ba, sai don a samu sukunin tabbatar da cikakken bincike. Yanzu haka dubun dubatan 'yan gudun hijira ne da ke bi ta kasashen yankin Balkan, suka shigo kasashen Austriya da Jamus. A baya bayan nan an samu rudani a kan iyakokin Kuretiya da Sloveniya. A kuma halin da ake ciki jihar Baveriya da ke kudancin Jamus ta zargi gwamnatin Austriya da kyale 'yan gudun hijira da suka shiga kasar ta Sloveniya, shigowa Jamus ba da wata matsala ba.