1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asalin Ebola

Adrian Kriesch / AS
January 14, 2015

A cikin shekara ta 1976 ne aka gano cutar Ebola.

https://p.dw.com/p/1EGjs
Hoto: picture-alliance/dpa

Kwayar cutar Ebola na da kankantar da ba za a iya ganinta da idanu ba, dole ne sai an yi amfani da na’ura kuma yanayinta kan kasance ne kamar zare. A shekarar 1976 ne masu bincike suka gano cutar a wani kauye da ke Zaire wadda yanzu ake kira Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango. An sanyawa cutar suna ne daga sunan wani kogi da ke kauyen da aka ganota wato kogin Ebola.

Cutar ta bayyana har sau uku a cikin shekarun 1970 a Zaire da Sudan sai dai ba a sake ganinta ba sai cikin shekara ta 1994. Bayyanar cutar ta Ebola a Gabun shi ne karon farko aka same ta a yankin yammacin Afirka.

Daga lokacin da aka gano ta zuwa yau an samu bayyanarta har sau 20, sai dai dukanninsu an yi kokari wajen kawar da su cikin gaggawa. Kafin wannan lokacin dai mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar ba su gaza 430. Bayyanar cutar da aka samu a wannan karon dai ta fara ne daga kasar Gini a karshen shekarar 2013, daga nan ne kuma ta yadu har ta zama annoba a kasashen da suka hada da Saliyo da Liberiya inda dubban mutane suka rasu yayin da wasu sama da dubu 10 suke dauke da ita.

Daya daga cikin dalilan da suka haddasa bazuwar cutar, ba tare da an dakile ta ba shi ne, kasashen duniya da kasashen da ta bulla ba su yi zaton annobar za ta iya yin ta’adin da ta yi yanzu ba.

Wani kwarare kan cutukan da ke saurin yaduwa a tarayyar Najeriya mai suna Oyewale Tomori ya ce "cutar ta riski mutane cikin rashin shiri da ma rashin amincewa da ita". Akwai abubuwa da dama da suka shige duhu, kuma har yanzu an gaza samun amsoshinsu, kamar irin abin da ke faruwa a jikin mai dauke da cutar, da dalilan da suka sanya masu kankantar shekaru suka fi jurewa cutar a kan wadanda suka manyanta. Shekaru 40 kafin wannan annobar mutane 2500 ne suka mutu, adadin da ya gota na wadanda suka kamu da cutar tarin fuka ko cutar AIDS ko SIDA a kullum. Wani abun har wa yau shi ne rashin kwarewa ta kasashen duniya wajen tunkarar annobar ta Ebola.

Tun bayan bullar annobar kwana-kwanan nan aka matsa kaimi wajen neman rigakafin cutar ko maganinta. Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) na fatan samar da rigakafin cutar ga dubban mutane a yankunan da ta fi shafa a tsakiyar shekarar 2015 yayin da ta ce tana son samar da rigakafin cutar har miliyan guda zuwa karshen 2015.