Zargin magudi a zaben fidda gwani ya sa babbar kotun Najeriya a jihar Adamawa ta soke tikitin takarar Sanata Aishatu Binani da tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu ya kalubalanta
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a 'Yola jihar Adamawa a Najeriya, ta soke tikitin takarar Sanata Aishatu Binani na neman kujerar gwamnan jihar a jam'iyyar APC a zaben 2023 saboda zargin magudin a zaben fidda gwani.
A hukuncin da ta yanke a yau Juma'a, kotun da ke karkashin Mai shari'a A.M Anka ta bukaci Binani da ta daina bayyana kanta a matsayin ‘yar takarar jam'iyyar APC a jihar.
Tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu, wanda ya fafata a zaben fidda gwani tare da Binani, ya shigar da kara, inda ya bukaci a soke zaben da aka gudanar a ranar 27 ga watan Mayu.