Angela Merkel tayi kira ga Palasdinwa da su amince da bukatun kasashen yamma | Labarai | DW | 31.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel tayi kira ga Palasdinwa da su amince da bukatun kasashen yamma

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta roki sabuwar gwamnatin Palasdinawa data sake duba bukatun kasasahen yammacin duniya,ta amince da kasancewar kasar Israila.

Tuni dama kasashan na yammam su jingina wannan sharadi ga gwamnatin ta Palasdinawa kafin su maida taimakon da suke bata.

A lokacin ganawarta da sarki Abdallah na Jordan Merkel ta yaba da yunkurin da kasashen larabawa sukeyi na farfado da shirin zaman lafiya na yankin gabas ta tsakiya.

A matsayinta ta shugabar kungiyar taraiyar turai Merkel tace zata bada fifiko kann batun zaman lafiya a yankin gabas ta tsaykiya.

Bayan ganawarta da shugaban na Jordan Merkel ta kama hanyarata zuwa Israila inda ake sa ran zata gana da Ehud Olmert da kuma shugaba Mahmud Abbas a yankin Palasdinawa.