Angela Merkel ta kare matsayinta kan ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 12.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel ta kare matsayinta kan 'yan gudun hijira

A wani yunkuri a yayin gudanar yakin neman kamfen na karshe na zabubbukan 'yan majalisun dokokin jihohi uku da ke a Gabashin Jamus.

Angela Merkel da ke zama shugabar gwamnatin kasar ta yi kokarin kare matsayinta t kan 'yan gudun hijira da ke ci gaba da shigowa kasar a inda ta ce:

''A wasu lokuta ya zama wajibi a dauki tsauraran hukunce-hukunce,a wani kaulin kusan dukkanin kasashen da ke a yankin Balkans sun taka rawa akan batun, kuma abubuwa masu tari yawa sun faru,yana da kyau mu koyi darasi daga kura-kuran da muka tafka a baya ta yadda abubuwa za su kai ga ingantuwa a gaba.''

Kazalika Shugabar ta kara da cewar mutane sun shigo mana kwatsam suna bukatar taimako idan muna da halin yin sai mutaima kesu:Angela Merkel dai na wadan nan kalaman ne a yayin ganagamin yakin neman zabe a Baden-Württemberg