1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kokarin sasanta Rasha da Ukraine

November 26, 2018

Manyan jami'an wasu kasashen Turai na wata ganawa domin nazarin sabon rikicin nan da ya taso tsakanin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/38v6c
Russland Konflikt Krim Ukraine | Ukrainische Schiffe im Hafen von Kerch
Hoto: picture-alliance/dpa/Tass/S. Malgavko

Manyan jami'an kasashen Jamus da Rasha da Ukarine da kuma Faransa na ganawa a birnin Berlin domin nazarin sabon rikicin nan da ya taso tsakanin Rasha da Ukraine.

Kasar Rasha dai na bijire wa kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi mata, na ta saki wasu jiragen ruwa mallakin kasar Ukraine.

Wasu jami'an Rashar ne dai suka harbi jiragen Ukraine a kan iyaka tare da kame wasu kusa da Crimea a karshen mako.

Ganawar a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus, za ta maida hankali ne kacokan a kan rigimar ta karshen mako, don ganin yadda za a iya kaiwa ga samun maslaha.