Ana ci gaba da neman mafita kan rikicin tattalin arzikin kasar Girka | Labarai | DW | 24.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da neman mafita kan rikicin tattalin arzikin kasar Girka

Kasar Girka da masu bai wa kasar rance suna sake ganawa domin magance matsalolin tattalin arziki da kasar take fuskanta

Firaminista Alexis Tsipras na kasar Girka yana neman cike gibi tsakanin gwamnatinsa da masu bai wa kasar rance, kan neman gudanar da karin sauye-sauye, kafin wa'adin mako mai zuwa.

Kafin tafiya zuwa birnin Brussels na kasar Beljim da ake ganawar, Firaminista Tsipras ya soki lamirin hukumar ba da lamuni ta duniya, IMF, saboda yadda take nuna rashin gamsuwa da sauye-sauyen da kasar ta gabatar. Kasuwannin hannuyen jari a kasashen Turai da Amirka na ci gaba da duba abin da ke faruwa, musamman bayan da kasashe masu ba da bashi suka yi watsi da matakan da kasar Girka ta yi alkawarin dauka. Bangarorin za su ci gaba da tattauna mafita domin magance matsalolin tattalin arziki da kasar ta Girka ta samu kanta a ciki.