Ana ci gaba da kokarin ceto ′yan matan Chibok | Labarai | DW | 25.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da kokarin ceto 'yan matan Chibok

A lokacin da yake jawabai a gaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya Shugaba Goodlck Jonathan na Najeriya ya ce hukumomi ba su gajiya ba a kokarin ceto 'yan matan.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya fada wa taron babbar mashawartar Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York cewa hukumomi a Najeriya na ci gaba da aiki tukuru don ceto 'yan matan nan su kimanin 200 da kungiyar Boko Haram ta sace daga wata makarantar sakadandare a tsakiyar watan Afrilu. Ya ce ko da yake fiye da watanni biyar ke nan da sace 'yan matan daga makarantar sakandaren ta Chibok, amma hukumomi ba sa nuna gajiyawa a kokarin da suke na ceto 'yan matan. Jonathan dai ya sha suka a cikin gida da kuma ketare dangane da jinkirin da aka samu wajen daukar matakai bisa manufar ceto 'yan matan da kuma kawo karshen ta'asar da kungiyar Boko Haram ke yi musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.