Ana bincike kan cin zarafin mata a Jamus | Labarai | DW | 08.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana bincike kan cin zarafin mata a Jamus

Mahukuntan Jamus za su dauki tsauraran matakai kan wadanda suka ci zarafin mata lokacin bikin shiga wannan sabuwar shekara ta 2016.

Mahukuntan kasar Jamus sun bayyana cewar daga cikin sunayen 31 na mutanen da ake bincike da cin zarafin mata lokacin bukukuwan shiga sabuwar wannan shekara ta 2016 a birnin Cologne, mutane 18 daga ciki sun kasance bakin haure da ke neman mafaka. Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ya tabbatar da haka.Shugabar gwamnati Angela Merkel ta yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin. Jam'iyyar mai mulkin kasar ta Jamus ta CDU wadda take taro a birnin Mainz ta bukaci a dauki tsauraran matakai kan wadanda aka samu da laifi. Kuma duk wanda aka samu da laifi daga cikin bakin haure da 'yan gudun hijira bayan hukunci zai rasa dama ta samun mafakan a cikin kasar ta Jamus.

Kimanin mata 121 suka ba da rohoto fuskantar cin zarafi a jajiberin shiga sabuwar shekara daga maza kimanin wadanda ake zargin sun fito daga kasashe Larabawa na Gabas ta Tsakiya gami da Arewacin Afirka.