An yi zanga-zangar nuna jimirin zaman tare a kasar Jamus
January 13, 2015Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da mambobin gwamnatinta sun shiga zanga-zangar nuna goyon baya zaman tare na addininai tare da girmama juna da ta gudana a wannan Talata a birnin Berlin fadar gwamnatin kasar.
Shugabannin Musulmai suka shirya zamga-zangar a kofar Brandenburg mai cike da tarihi inda aka girmama wadanda hare-haren Faransa suka yi sanadiyar hallaka su a makon jiya. Zanga-zangar an yi karkashin taken "Mu tsaye tare wa juna, ta'addanci ba da sunanmu ba."
Shugaban Jamus Joachim Gauck yana cikin wadanda suka yi tattakin domin nuna yadda kasar take runguman mabanbantan al'adu da addinai.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal