An yi wa mayakan IS kawanya a Siriya | Labarai | DW | 18.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi wa mayakan IS kawanya a Siriya

Dakarun gwamnatin Siriya da ke samun goyon bayan rundunar sojin Rasha sun sanar da yi wa yankin Okayrbat da ke karkashin ikon mayakan IS kawanya.

A wata sanarwar da ma'aikatar tsaron Rasha ta fitar ta ce rundunar sojin sun karbe ikon mashigar da mayakan ke amfani da shi wajen shigar da makamai a cikin Siriya. Sanarwar ta kara da cewa rundunar sojin Rasha da ke taimaka wa gwamnatin shugaba Bashar al-Assad ta kaddamar da wani hari a maboyar mayakan da zimmar lalata manyan motoci da makamai da IS ke amfani da su wajen kai hare-hare na ta'addanci.

Dakarun Siriya sun kuma yi ikirarin samun nasara a kokarin da suke na murkushe kungiyar da ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a kasar.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syrian Observatory ta tabbatar da labarin yi wa mayakan na IS kawanya a sanarwar da ta fitar a wannan Juma'ar.