An yi magudi a zaben Nijar | Labarai | DW | 30.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi magudi a zaben Nijar

Jam'iya mai mulki ce ke sahun gaba a alkaluman sakamakon zaben da hukumar zabe ta Nijar wato CENI ta bayyana.

Alkalumman sakamakon zaben da ake cigaba da samu a Jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa Jam'iya mai mulki ce ke kan gaba da gaggarumin rinjaye.

Jam'iyar PNDS da tsohon ministan harkokin cikin gida Bazoum Muhammed ke wa takara, ita ce ke kan gaba daga cikin sakamakon da hukumar zaben kasar ta CENI ta bayyana. Babban abokin hamayarsa Mahammane Ousmane shine ke maye masa baya.

Hukumar zaben ta ce zata cigaba da sanar da sauran sakamakon da zarar ya kammala, idan kuma daga karshen sakamakon aka gaza samun dan takarar da ya samu abin da ake bukata, to la budda sai an koma rufunan zabe.

Tawagar masu sa ido da kungiyar Tarayyar Afirka ta tura domin sa ido a zaben ta bayyana sahihancinsa, sai dai dan abinda ba a rasa ba in ji jami'an. 

'Yan adawa a nasu bangaren sun ce jam'iya mai mulki ta tafka magudi.