Zanga-zangar Hong Kong na kara zafi
September 7, 2019Talla
Jami'an 'yan sanda sun sanya shinge a tashoshin jiragen kasa da motocin haya don samun gudanar da binciken kwakwaf a fadin yankin. A ranar Larabar da ta gabata ne jagorar yankin Carrie Lam ta sanar da shirin janye dokar da ta haifar da sabani tsakanin gwamnati da mazauna yankin, yunkurin da masu zanga- zangar suka yi watsi dashi.
Daga cikin shugabannin da suka sanya baki domin kawo karshen wannan danbarwa dai har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wacce ta jaddada bukatar martaba 'yancin al'ummar yankin na Hong Kong yayin ziyarar da take a yanzu haka a China.