1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsagaita bude wuta a rikicin Libiya

Abdul-raheem Hassan
January 12, 2020

Gwamnatin hadin kan kasa a Libiya ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da dakarun sojin Janar Khalifa Haftar da ke kan bakansu na kwace iko da Tripoli babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3W4BP
Bildkombo Haftar und as-Sarradsch

Bangarorin biyu da suka dau lokaci suna gwabza fada kan iko da Tripoli sun cimma matsaya ta dakatar da fada bayan wata yarjejeniya da kasashen Turkiyya da Rasha suka taimaka aka cimma.

Sai dai Janar Haftar ya ja kunnen bangaren gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya kan su guji tada rikici nan gaba in ba haka ba za su su fuskanci martani mai tsanani.