An soma taron ƙungiyar ƙasashen G7 | Labarai | DW | 07.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An soma taron ƙungiyar ƙasashen G7

Shugabannin ƙasashen masu ƙarfin tattalin arzikin masana'antun na yin nazarin batutuwa da dama a Elmau da ke a kudanci Jamus.

Manyan batutuwa da taron ke dubawa sune batun rikicin Ukraine da na matsalar kuɗi da Girka ke fuskanta.Sannan kuma an tsara taron zai taɓo batun kasuwanci da ɗumamayar yanayi da kiwon lafiya da maganar yaƙi da talauci da kuma samar da tsaro.

To sai dai masu fafutuka da ke yin zanga-zanga sun yi yunƙurin datse hanyoyin da ke zuwa zauren taro da ke a Elmau.Abin da ya tilasta wa wasu shugabannin isa wurin ta jiragen sama masu saukar ungulu.