Jagoran 'yan adawa ya ayyana lashe zaben Kamaru
October 14, 2025
Jagoran 'yanadawa na kasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Lahadi da ta gabata 12 ga watan Oktoba da muke ciki.
Matsayin jagoran 'yan adawa
A cikin wani jawabi da ya gabatar Tchiroma Bakary ya bukaci ganin an mutunta zaben da 'yan kasa suka yi.
Mai shekaru 76 da haihuwa Tchiroma Bakary ya bukaci Shugaba Paul Biya ya rungumi kaddara na faduwa a zabe. Shi dai jagoran 'yan adawan ya shafe shekaru da dama a matsayin minista a gwamnatin ta Biya.
Zai dauki makonni biyu kafin sanin sakamakon zaben kasar ta Kamaru inda Shugaba Biyu mai shekaru 92 kuma wanda ya fi kowanni shugaba a duniya tsufa, yake neman fadada mulkin na tsawon shekaru 43 da wani sabon wa'adin mulkin shekaru bakwai, a wa'adi na takwas.