Issa Tchiroma Bakary dan siyasa ne a Kamaru wanda ya taba zama dan majalisa, sannan daga bisani ya rike mukamin minista so da dama.
Shi wannan Injiniya ya yi fafutuka wajen ganin demokaradiyya ta kafu a Kamaru. Sai dai daga baya jam'iyyarsa ta kulla kawance da gwamnatin Shugaba Paul Biya, lamarin da ya ba shi damar rike mukamun ministan sufuri da na yada labarai, kana kakakin gwamnati.