An saki Faransawan da aka sace a Nijar | Labarai | DW | 29.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki Faransawan da aka sace a Nijar

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce kungiyar Al-ka'ida reshen arewacin Afirka ta saki Faransawa uku da aka kama shekaru uku da suka gabata a yankin Arlit.

This image taken from video and provided by U.S.-based SITE Intelligence Group Thursday Sept. 30, 2010 shows the first images of a group of foreign hostages working for a French energy company who were seized in Niger two weeks ago by an al-Qaida offshoot, according to the group that monitors terrorism. The hostages were grabbed in the middle of the night on Sept. 16 from their guarded villas in the uranium mining town of Arlit in Niger where they worked for French nuclear giant Areva. Five are French citizens, the other two are from Togo and Madagascar. (AP Photo/SITE) ** EDITORIAL USE ONLY **

Faransawan da aka sace a yankin Arlit

Da ya ke magana wa manema labarai a kasar Silovakiya inda ya ke wata ziyarar aiki, Hollande ya jinjinawa shugaban Nijar Mouhamadou Issoufou, saboda rawar da ya taka wajen sakinsu da aka yi.

Mr. Hollande ya kuma ce yanzu haka ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius da takwaransa na tsaro Jean-Yves Le Drian, na kan hanyarsu ta zuwa kasar Nijar, domin dawo da mutanen gida Faransa, nan ba da dadewa ba inda a sada su da iyalansu.

An kame Fransawan hudu ne a ranar goma ga watan Satumbar shekara ta 2010, lokacin da suke yi wa kamfanin hakar karfen Uranium din nan na Areva mallakar kasar ta Farnsa aiki a yakin Arlit da ke arewacin Jamhuriya ta Nijar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman