An sake samun fashewar wani abu a Jamus | Labarai | DW | 27.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake samun fashewar wani abu a Jamus

Yankin kasar Jamus da lamarin ya faru ya kasance inda aka samu hare-hare makon da ya gabata abin da ya kai ga mutuwar mutane sama da 10.

An samu fashewar wani abu kusa da cibiyar rijistar 'yan gudun hijira da ke garin Zirndorf kusa da birnin Nuremberg a Arewacin Jihar Bavaria da ke kasar Jamus. 'Yan sanda sun ce wani karamin akwati ne ya tarwatse a kofar shiga ginin. Babu wanda ya samu rauni sakamakon faruwar lamarin. Tuni 'yan sandan kasar ta Jamus suka kaddamar da bincike. Cikin kwanakin da suka gabata dai, an samu hare-hare a wannan yankin na Jamus da ya kai ga mutuwar mutane sama da 10 kana wasu da dama suka jikkata. Ita dai kasar ta Jamus ta karbi 'yan gudun hijira galibi daga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya fiye da milyan guda a shekarar da ta gabata ta 2015.