An sace wani ɗan ƙasar China a Najeriya | Labarai | DW | 24.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace wani ɗan ƙasar China a Najeriya

'Yan sanda a Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga waɗanda ba a shaida su ba sun sace wani ɗan kasar China a jihar Kogi da ke a yankin tsakiya na ƙasar.

Wani kakakin 'yan sandar na jihar Elvis Aguebor ya shaida wa manema labarai cewar mutumin wanda ma,aikaci ne a ma'aikatar ruwa ta gwamnati,an sace shi tun ranar Talata.

Kuma mutanen da ke ɗauke da makamai sun taras da shi a gidansa idan suka yi awan aba da shi.Tun da farko sai da maharan suka yi harbi cikin iska kafin su tafi da shi.A ranar Lahadin da ta wuce ma, wasu 'yan bindigar sun kai famarki a kan wani ofshin 'yan sanda a jihar.