1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabunta kwamitin gudanarwar majalisar Nijar

Gazali Abdou Tasawa
April 6, 2023

A wannan Alhamis (6.4.2023) ne majalisar dokokin janmhuriyar Nijar ta bude babban zaman taronta na farko na shekara a birnin Yamai.

https://p.dw.com/p/4PnbY
Zauren majalisar dokokin Nijar
Zauren majalisar dokokin NijarHoto: Gazali A. Tassawa/DW

A wannan zama majalisar dokokin kasar ta Nijar za ta yi nazarin wasu sabbin dokoki da gwamnati ta shigar a gabanta da kuma sabunta kwamitin gudanwarwar majalisar. Sai dai batun tsaro da neman yin gyaran fuska ga dokar tsarin tafiyar da jam'iyyu domin rage yawansu a kasar na daga cikin batutuwan da suka mamaye bikin bude taron.

An bude zaman majalisar na yau da taken kasar a karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin Nijar Alhaji Seini Omar, inda za ta yi nazarin jerin dokokin da gwamnatin kasar za ta shigar a gabanta da kuma sabunta mambobin kwamitin gudanarwa na majalisar.

Sai dai a jawabinsa na bude taro shugaban majalisar dokokin kasar ta Nijar Honnorable Alhaji Seini Omar ya jinjina wa shugaban kasa Mohamed Bazoum da gwamnatinsa da ma sojojin kasar kan kokarin da suke a fannin yaki da ta'addanci. Sai dai kuma ya bukaci shugaban kasa da ya kara kaimi a cikin kokowar ya na mai cewa:

Shugaban majalisar Nijar Seini Oumarou
Shugaban majalisar Nijar Seini OumarouHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

"Majalisar dokokin kasa na kira ga shugaban kasa Mohamed Bazoum da ya fadada a fannin yaki da ta'addanci mu'amalar Nijar da duk kasashe mokwabtanmu domin kafa kawance mai karfin da ya zarce na G5 Sahel. Kuma a game da sabbin muggan ayyukan tsageranci da suka bayyana a wasu yankunan kasar, majalisa na kira ga shugaban kasa da ya gaggauta daukar matakan dakile su. Domin idan aka bari suka samu gindin zama za su kasance hadari fiye da ta'addanci, kuma mu da samin zaman lafiya har abada".

Sai dai da yake tsokaci kan batun tsaron Honnorable Laouali Ibrahim Maijirgui bayanai ya yi kan barazanar  tsaron da ke addabar jihar Maradi da har yanzu gwamnati ba ta shawo kanta ba.

Wani batun da ya mamaye bikin bude zaman majalisar shi ne gargadin da shugaban majalisa ya yi ga yadda kansaloli ke tafiyar da aikinsu a kasar. Honnorable Sani Boukari Zilli ya yi mana karin bayani kan wannan matsala da majalisar dokokin kasar ke son dubawa a wannan zama na ta.

Shugaba Bazoum Mohamed
Shugaba Bazoum MohamedHoto: Niger Prasidential Website

Wani batun na daban da majalisar ke son dubawa a wannan zama shi ne na yin gyaran huska ga dokar tsarin tafiyar da jami'iyyun siyasa a kasar kamar dai yadda Honnorable Lantana Oumarou ta yi mana karin bayani.

Majalisar dokokin kasar ta Nijar za ta share watanni uku tana wannan zama nata inda baya ga yin dokoki da gayyato ministoci domin neman bahasi kan wasu matsaloli da ke addabar kasar, za ta sabunta kwamitin gudanarwarta kamar yadda doka ta tanada amma ban da shugaban majalisar dokoki wanda ke da wa'adin shekaru biyar.