Seini Oumarou dan siyasa na Jamhuriyar Nijar wanda ya rike mukamai daban-daban na gwamnati, kana ya yi takarar shugabancin kasa.
Daga cikin mukaman da ya rike akwai minista a ma'aikatu daban-daban kafin zama firaminista karkashin gwamnatin Tandja Mamadou. Haka kuma ya zama shugaban majalisar dokoki kafin juyin mulkin da sojoji suka yi a shekara ta 2010.