An nada sabbin ministoci a Najeriya | Labarai | DW | 05.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada sabbin ministoci a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan ya sanar da nadin Aliyu Gusau a matsayin sabon ministan tsaro da Aminu Wali na hulda da kasashen waje, sai Boni Haruna a ma'aikatar matasa.

Lawrencia Laraba ita ce sabuwar ministar kula da muhalli. Asabe Asama'u Ahmed ce karamar ministar kula da ayyukan gona, kana Akon Eyakenyi ta kasance ministar kula da mnada sabbin ministociuhalli, sai Abduljelili Adesiyan a matsayin ministan harkokin 'yan sanda.

Sauran ministocin sun hada da Musiliu Obanikoro karamin minista a ma'aikatar tsaro, Muhammed Wakil minista a ma'aikatar makamashi, a yayin da Khaliru Alhassan ya samu karamin minista a ma'aikatar lafiya ta tarrayr Najeriya.

A yau din ne kuma shugaba Jonathan ya cire ministan wasanni, Bolaji Abdullahi, inda nan take aka maye gurbinsa da Tamuno Danagogo.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal