An koma gumurzu a Yemen bayan dakatar da shawarwari | Labarai | DW | 09.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma gumurzu a Yemen bayan dakatar da shawarwari

Kawancen sojojin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun yi lugudan wuta a birnin Sanaa na kasar Yemen.

Bayan rugujewar tattaunawar neman zaman lafiya a Yemen, a karon farko cikin watanni, kawancen sojojin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun sake yin lugudan wuta kan Sanaa babban birnin Yemen. Likitoci sun ce akalla fararen hula 14 ne suka rasu sakamakon ruwan bama-baman. Da farko dakarun gwamnatin shugaba Abd-Rabbu Mansur Hadi da kasashen duniya suka amince da ita, sun kaddamar da wani farmaki na sake kwace iko da birnin da ya fada hannun 'yan tawayen Shi'a na Houthi shekaru biyu da suka wuce.

A karshen mako wakilan Houthi da ke samun goyon bayan Iran da na gwamnatin Hadi sun hadu a Kuwaiti don tattauna batun neman zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke shiga tsakani. Sai dai an dakatar da shawarwarin, tun sannan ne kuma fadan ya kara rincabewa. Tun a shekarar 2015 kawancen sojojin da Saudiyya ke wa jagora ke mara baya ga dakarun Hadi wajen kai farmaki ta sama.