An kawo gawarwakin ɗaliban jamus gida. | Labarai | DW | 10.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kawo gawarwakin ɗaliban jamus gida.

Ɗaruruwan jama'a sun taru a bakin makarantar da ɗalibban ke karatu kafin mutuwarsu domin tarben gawarwakin tare da zuba furanni na nuna alhini.

A ƙasar Jamus a wannan laraba ne aka kawo gawarwakin ɗalibban nan 16 na ƙasar waɗanda suka rasu a cikin haɗarin jirgin kamfanin Germanwings na ƙasar ta Jamus da ya wakana a watan Mars ɗin da ya gabata a cikin tsaunikan Alpes na ƙasar Faransa.Da misalin ƙarfe huɗu da minti 40 na yammacin yau ne dai aka iso da gawarwakin ɗalibban da mallamansu biyu a yammacin ƙasar ta Jamus inda ɗaliban ke karatu kafin mutuwar tasu.

Mutane 150 ne da suka haɗa da 72 na ƙasar Jamus 50 'Yan ƙasar Spain suka hallaka a cikin haɗarin jirgin saman wanda ya wakana a ranar 24 ga watan Mars ɗin da ya gabata.