An kashe wata ′yar majalisar Burtaniya | Labarai | DW | 16.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wata 'yar majalisar Burtaniya

An dakatar da kamfe din da ake yi kan zaben raba gardama na ficewar Burtyaniya daga EU bayan da aka hallaka wata 'yar majalisa ta jam'iyyar Labour da ke adawa.

'Yar majalisar mai suna Jo Cox ta gamu da ajalinta ne bayan da wani mutum ya harbe ta kana ya daba mata wuka a yankin Birstall da ke kusa da Leeds daidai lokacin da ta ke shirin fara wani taro da jama'ar da ke mazabarta.

Firaministan Burtaniya din David Cameron ya ce kisan Ms. Cox, yar shekaru 41 da haihuwa abin takaici ne ga kasar baki daya. Jami'an 'yan sanda sun ce sun kame wani mutum da ake zargi da kisan 'yar majalisar.

Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin kisan matar ba sai da bayanai sun nuna cewar ta na daga cikin 'yan siyasar da ke goyon bayan cigaba da kasancewar Burtaniya a cikin kungiyar EU.