An kashe wasu sojojin Nijar a Diffa | Labarai | DW | 18.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wasu sojojin Nijar a Diffa

Akalla wasu sojojin Nijar guda shida ne suka mutu bayan da motarsu ta taka nakiya ta kuma fashe a yankin gudu maso gabashi na jihar Diffa kan iyaka da Najeriya wanda ke fama da rikicin Boko Haram.

Magajin garin Kabalewa Abari Elhaji Dauda ya ce lamarin ya faru tun a ranar Asabar a kusa da garin Kabalewar.A halin da ake ciki kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce da ita da Nijar ɗin sun yi nasarar sake buɗe makarantu boko 99 cikin 166 waɗanda aka rufe a jihar ta Diffa saboda tashin hankalin na Boko Haram.

Shirin na sake buɗe makarantu wanda aka soma tun a cikin watan Nuwamba da ya gabata ,ya sa ya zuwa yanzu yara kusan dubu shida maza da mata sun sake komawa makaratun.Hukumar yara kanana ta MDD UNICEF ta ce sama da makarantu dubu biyu aka rufe a Nijar da Najeriya da kuma Kamaru saboda hare hare na Boko Haram.