1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Horst Seehofer ya yi tsokaci a kan kisan wani dan siyasa

Abdourahamane Hassane
June 18, 2019

Ministan cikin gida na Jamus Horst Seehofer ya ce mutuwar wani dan siyasa dan jam'iyyar CDU Walter Lübcke wanda ke goyon bayan kwararrar 'yan gudun hijira na kan hanyar tabbatar da cewar kasheshi aka yi.

https://p.dw.com/p/3Kdnn
Walter Lübcke Regierungspräsident von Kassel
Walter Lübcke dan siyasa kana babban jami'in gwamnatiHoto: picture-alliance/dpa/U. Zucchi

A halin da ake ciki  'yan sanda na tsare da wani mutumin da ake zargi wanda ya taba kai hari a wani sansanin 'yan gudun hijira a shekara ta 1993 dan jam'iyyar NPD, ta masu ra'ayin 'yan Nazi. Mutumin da aka kashen Walter Lübcke dan kimanin shekaru 65 da haifuwa an taras da gawarsa a kan filin gidansa a Wolfhagen da ke cikin Jihar Hessen da ke a yankin tsakiya maso yammaci na Jamus a farkon wannan wata na Yuni. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi Allah wadai da harin da ta ce abin takaici ne.