An kamalla zaben yan majalisun dokoki a Masar | Labarai | DW | 07.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kamalla zaben yan majalisun dokoki a Masar

A kasar Masar an kammala zagayen karshe na zaben yan majalisar dokoki.

Saidai wannan zagaye, ya fuskanci tashe tashe hankulla, a wurare daba daban.

Rahotani daga kasar sun ambato cewa, a kalla mutane 3 su ka rasa rayuka yau, da dama kuma sun ji raunuka,a sakamakon harben harben jami´an tsaro.

Kungiyar yan uwa musulmi ta dangata, hargitsin da salon magudi, don taka birki gay an takara da ta jera.

A rufunan zabe da dama jami´an yan sanda sun yi anfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa mutanen da su ka zo zabe, kazalika a wasu wuraren kwata kwata, sun hana jama´ata yi zaben.

A jimilce, kujerun yan majalisa 120 ne ,a ka zaba yau domin cika gurbin jimilar kujeru 454 da majalisar ta kunsa.

Ya zuwa yanzu, daga wannan kujeru, 454, kungiyar yan uwa musulmi ta lashe 76.

A cikin lissahi da ta yi, ta na hasashen samu Karin wasu kujeru 15 zuwa 20 a zaben na yau.

Saidai duk da wannan nasara, jam´iyar PND ta shugaba Osni Mubarak, ta samu babban rinjaye a Majalisa.

Kungiyoyin kare hakokin bani adama, da su ka iddo ga zaben sun yi Allah waddai da wala walar da ke cikin sa , wadda gwamnati ta shirya, domin kwashe dukkan kujerun da su ka rage a Majalisa.