1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama makamai bayan kashe 'yan sandan Jamus

Abdul-raheem Hassan
February 1, 2022

Jami’an binciken kwakwaf da ke bin diddigin kashe 'yan sanda biyu a yammacin Jamus a ranar 30 ga watan Janairun 2022, sun kama manyan makamai a gidajen mutanen da ake zargi da aikata kisan.

https://p.dw.com/p/46NH2
Deutschland Messerangriff im ICE zwischen Regensburg und Nürnberg
Hoto: Ayhan Uyanik/REUTERS

A cewar majiyoyin tsaro, ‘yan sanda sun gano bindigogi guda biyar da wasu dogayen bindigu guda 10 da harsasai masu yawa a lokacin gduanar da bincike a wani gida a garin Spiesen-Elversberg, wani karamin gari a Saarland d ake gundumar Neunkirchen a yammacin Jamaus.

Masu binciken sun gano wasu dogayen bindigu guda biyu a gidan mutum na biyu da ake zargi shima yana da hannu a kisan 'yan sandan, an kuma ce mutumin mai shekaru 32 ya bayyana aniyarsa ta bayar da shaida kan abin da ya faru.

Masu binciken sun yi zargin cewa wani mutum mai shekaru 38, wanda shi ma ake zargi da aka kama shi tun ranar da lamarin ya faru, na da masaniya kan makaman da aka samu a wurin binciken.

A safiyar ranar Litinin ne 'yan bindiga suka harbe wata ‘yar sanda mai shekaru 24 da abokin aikinta mai shekaru 29 a gundumar Kusel da ke kusa da Kaiserslautern, bayan tsayar motar su. Kafin su mutu, sun iya yin magana da rediyon oba-oba da abokan aikinsu, suna cewa "Suna harbi.