1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari da wuka a cikin bas a Jamus

Abdul-raheem Hassan
July 20, 2018

'Yan sanda sun kama maharin da ya jikata mutane 14 a cikin motar bas a birnin Luebeck da ke jihar Schleswig-Holstein a arewacin Jamus.

https://p.dw.com/p/31qGP
Messerattacke in Lübecker Linienbus
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Scholz

Wadanda suka shaida lamarin sun ce maharin ya zare wuka yayin da motar ke cike da mutanen da ke tafiya bakin ruwa a kusa da birnin Luebeck, inda fasinjoji suka rika tsalle daga motar bayan da direban ya tsaya domin ba wa fasinjoji damar tserewa. Kawo yanzu dai babu rahotannin asarar rayuka daga harin, amma wasu mutane biyu na cikin mawuyacin hali.

Babu karin bayani kan maharin ko musabbabin kai harin daga hukumomin tsaro, amma a cewar jaridar Luebecker Nachrichten "Ana zargin maharin dan kasar Iran ne mai kimanin shekaru 30." Tuni dai 'yan sandan yankin suka baza jami'ansu inda abin ya faru domin kare lafiyar al'uma, tare da zurfafa bincike kan harin. Hukumomin Jamus dai sun nesanta harin da ta'addanci.

Sai dai dama Jamus na cike da fargabar barazanar kafin hare-hare tun bayan da kungiyar IS ta dau alhakin munanan hare-hare a fadin kasar a shekarun baya, ciki har da harin mota da ya kashe mutane 12 a kasuwar Kirsimeti a 2016.