An hari motar Dortmund ne don samun kudi | Labarai | DW | 21.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An hari motar Dortmund ne don samun kudi

Masu aikin bincike a Jamus sun ce mutumin da ya kai hari kan motar Kungiyar Dortmund a makon jiya ya kai harin ne da nufin karya darajar hannayen jarin kungiyar da kuma samun riba a kasuwar hada-hadar kudi.

A kasar Jamus masu aikin bincike a game da mutuman nan na aka kama a wannan Jumma'a a bisa zargin kai hari kan motar kungiyar kwallon kafar Dortmund a makon jiya, sun bayyana cewa sakamakon binciken nasu ya gano cewa mutuman ya kai harin ne da nufin arzuta kansa ba wai da nufin ta'addanci ba kamar yadda aka zata da farko. 

Mahukuntan shari'ar kasar ta Jamus sun bayyana cewa mutuman mai suna Sergej W dan asalin kasar Rasha mai takardun zaman dan kasa a Jamus dan shekaru 28 ya saye kwanaki kalilan kafin wasan hannun jarin Kungiyar har dubu 15.

 A don haka ne ya kai hari kan motar Kungiyar ta Dortmund don haddasa faduwar darajar hannun jarinta a kasuwar hada-hadar kudi, lamarin da zai ba shi damar cin kazamar riba da ta kai ta miliyan kusan hudu na Euro. Yanzu haka dai darajar hannun jarin kungiyar ta Dortmund ya fadi da kashi 5,5% tun bayan afkuwar lamarin.