An gaza samun daidaito a Jamus | Labarai | DW | 01.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gaza samun daidaito a Jamus

Ƙawancen jam'iyyun siyasa da ke yin mulkli a Jamus sun gaza cimma matsaya kan manufofin 'yan gudun hijira a ƙasar

Bayan taron kwanaki biyu da aka gudanar tsakanin shugabar gwamnati kuma 'yar jam'iyyar CDU Angela Merkel da shugaban CSU kuma Firimiyyan jihar Bavariya Horst Seehofer da kuma shugaban SPD kuma mataimakin shugabar gwamnati Sigmar Gabriel.

Kakin gwamnatin Steffen Seitbert ya ce an amince da wasu batutuwa da dama,amma ya ce har yanzu akwai saɓani kan batun kafa sansanonin wucin gadi na karɓar 'yan gudun hijira a kan iyakokin Jamus.Yazuwa yanzu an dai ɗage tattaunawar har zuwa ranar Alhamis mai zuwa.