1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara taron Berlin kan rikicin Libiya

January 19, 2020

Taron kolin nan da ke da manufar kawo karshen rikicin da ke ci a Libiya, ya yi kiran a gaggauta dakatar da kai hare-hare kan tashohin mai a gabashin Libiya.

https://p.dw.com/p/3WQyQ
Libyen-Konferenz in Berlin l Kanzlerin Angela Merkel und Präsident Macron
Hoto: Reuters/M. Tantussi

Shugabannin kasashe musamman wadanda ake ganin ke goyon bangaren tawaye da Khalifa haftar ke jagoranta, sun fara taron ne a Berlin fadar gwamnatin Jamus.

Sai dai fa jagoran gwamantin da duniya ta amince da ita a Libiyar Fayez al Sarraj,  na dora ayar tambaya kan ajendojin Khalifa Haftar, tun ma kafin a fara taron.

Taron na birnin Berlin kamar yadda aka nunar, na da burin kawo karshen takaddamar ne tare ma da hana shigar da makamai a Libiya.

Rikicin siyasa dai ya barke ne a Libiya a shekara ta 2011, matsalar da ta kai ga kisan tsohon Shugaba Moamar Ghaddafi.