An fara aikin gano asalin matan da aka ceto daga dajin Sambisa | Labarai | DW | 29.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara aikin gano asalin matan da aka ceto daga dajin Sambisa

Hukumomi a Najeriya na aikin tantance asalin daruruwan matan da aka kubutar daga hannun kungiyar Boko Haram.

Mahukunta a tarayyar ta Najeriya sun ce suna aikin tantance asalin 'yan mata da kuma mata kusan 300 da aka ceto daga hannun Boko Haram. Rundunar kasar dai ta ce ba bu 'yan matan Chibok daga cikin 'yan mata 200 da aka ceto daga dajin Sambisa. Sai dai kakakin ma'aikatar tsaron Najeriya ya yi kashedi da a guji yin riga malam masallaci, domin har yanzu ana cikin binciken dukkan matan da aka ceto daga dajin na Sambisa.

Shugabannin al'umma a garin Chibok sun fusata da sanarwar baya bayan nan wadda ta zo bayan da rundunar soji ta yi amai ta lashe daga furucinta na farko cewa an saki wasu daga cikin 'yan matan kuma ta san wurin da suke.

A yammacin ranar Talata kakakin ma'aikatar tsaro Chris Olukolade ya sanar cewa dakarun Najeriya sun ceto 'yan mata 200 da kuma mata 93 daga dajin Sambisa da ke jihar Borno.

Akalla mata 2,000 rahotanni suka ce Boko Haram ta yi garkuwa da su daga farkon shekarar bara.