An daure dan gudun hijira kan kisa a Jamus
September 3, 2018Talla
An yanke hukuncin ne a wata kotu a birnin Landau da ke Kudu maso yammacin Jamus. sai dai babu karin bayani kan dan gudun hijiran Abdul D, sai dai wasu bayanai na danganta wanda ya aikata kisan da dan kasar Afganistan da ke neman mafakar siyasa a Jamus.
Hukuncin ya zo ne a daidai lokacin da ake kokarin kwantar da zanga-zangar nuna kin jinin baki a garin Chemnitz da ke gabashin kasar bayan da wasu 'yan gudun hijira biyu suka kashe Bajamushe da wuka.
Dama dai kasar na cikin rudani kan tsarin bude kofa ga dubban 'yan gudun hijira, inda ko a baya-bayannan sai da aka samu rarrabuwar kawuna a cikin jam'iyyun hadaka da ke mulki kan batun 'yan gudun hijira.