An damke masu shirin ta′addanci a Jamus | Labarai | DW | 13.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An damke masu shirin ta'addanci a Jamus

Sama da 'yan gudun hijira miliyan guda sun shiga Jamus inda a cikinsu ake zargi akwai bara gurbi, da ke fakewa da neman mafakar siyasa dan aika-aika.

Thomas de Maiziere PK Razzia NRW in Berlin

Ministan harkokin cikin gidan JamusThomas de Maiziere

Wasu masu neman mafakar siyasa uku a Jamus sun zo hannun mahukunta a bisa zargin shirye-shirye na kitsa kai harin ta'addanci a madadin Kungiyar IS, an kuma gano cewa suna da alaka da harin da aka kai a birnin Paris na kasar Faransa a cewar ministan harkokin cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere.

Da yake jawabi a ranar Talatan nan de Maiziere ya ce tsawon watanni uku da aka dauka ana bincike an gano cewa mutanen masu shekaru 17 da 18 da 26 sun sami dama ta shigowa Turai ne ta hanyar masu fasakauri da suka shigo da wadanda suka kai hari a Paris a watan Nuwamba, harin da ya yi sanadi na kisan mutane 130. Kuma takardun bogi da suka yi amfani da su dan shigowa Turai an yi su a wuri guda.