An dage gasar zakarun Turai daga Rasha | Labarai | DW | 25.02.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage gasar zakarun Turai daga Rasha

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta dage wasan karshe na gasar zakaru da ya kamata a gudanar a St Petersburg na rasha zuwa paris, Faransa.

A wata sanarwar da ta fitar hukumar gudanarwar kwallon kafar Turan ta ce ga 'yan klub klub na kasashen Ukraine da Rasha, da ke muradin shiga kasar zakarun Turan, za su gudanar da wasan a wasu filaye na daban amma ba cikin kasashen ba.

Bugu da kari za ta bada goyon bayanta ga dukkan kokarin kwashe 'yan wasa da iyalansu da ke fuskantar barazanar tashin hankali da watsawe a Ukraine.

A ranar 28 ga watan mayu ne dai aka tsayar don gudanar da gasar karshe na UEFA  a katafaren filin wasa da ke St Petersburg na Rasha, inda ake saran halartar dubban daruruwan masoya wasannan kwallon kafa.