An ci zarafin mata a birnin Kolon na Jamus | Zamantakewa | DW | 06.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An ci zarafin mata a birnin Kolon na Jamus

lamarin ya auku a daren jajibiren sabuwar shekara, inda wasu maza matasa kimanin dubu daya suka dinga tare mata a tashar da ma wasu wurare na birnin suka dinga tsokanarsu tare da cin zarafin wasu a jikinsu.

Yanzu haka dai komai ya koma kamar yadda aka saba a babbar tashar jirgin kasa ta birnin Kolon kwanaki kalilan bayan wani lamari da ya auku a daren jajibiren sabuwar shekara, inda wasu maza matasa kimanin dubu daya suka dinga tare mata a tashar da ma wasu wurare na birnin suka dinga tsokanarsu tare da cin zarafin wasu a jikinsu.

Kwanaki kalilan bayan aukuwar wannan lamari a daren jajibiren shiga sabuwar shekara, matafiya da 'yan yawon bude ido da sauran masu gudanar da harkokinsu a babbar tashar jirgin kasar ta birnin Kolon na ci gaba da harokinsu. Sai dai har yanzu ana cikin kaduwa na aukuwar wannan lamarin inda aka ci zarafin wasu mata a tashar.

Shaidun gani da ido sun nuna damuwa kan lamarin

Deutschland Silvesternacht vor dem Hauptbahnhof in Köln

A yayinda tsageru suka tare hanya a birnin Kolon

Wani matashi da ke aiki a wani wurin sayar da abinci a tashar jirgin kasar ta Kolon wanda kuma ya shaida abin da ya faru ya ce bisa al'ada ranar jajibiren shiga sabuwar shekara tashar na cika makil da jama'a, amma abin da ya ga matasan sun yi a daren Alhamis ya wuce tunanin duk wani dan Adam mai cikakken hankali:

"Dukkansu sun kasance wasu masu cin zali, sai ihu da hayaniya kake ji a tashar. Wani yanayi ne mummuna hatta ga masu aiki a tashar. Mazan kawai muka gani a wajen tashar suna tashin hankali suna jifan mutane da kwalabe da kayan wasan wuta."

Matashin a tsawon rayuwarsa bai taba ganin irin wannan abu mai tashin hankali ba. Wata matashiya mai kiosk a tashar inda matafiya ke yawaitar sayen kaya, ta ce ita kam ta yi sa'a domin a wannan dare ba ta yi aiki ba, amma ta kadu musamman dangane da labarin cin zarafin mata da aka yi a gaban kiosk dinta. Ta ce daga yanzu saboda tsoron abin ka iya faruwa ba za ta sake yin aiki a karshen mako ko lokutan bikin Karneval ba, inda tashar kan cika da jama'a.

"Da rana abin da dan sauki kuma kana ganin jami'an tsaro da yawa na sintiri. Amma gaskiya ba ni da sha'awar yin aiki da yamma."

Tsagerun da suka ci zarafin matan sun faskari 'yan sanda

Rahotannin dai sun ce a daren jajibiren shiga sabuwar shekara, maza matasa kimanin dubu daya ne suka taru a gaban babbar tashar jirgin kasar ta Kolon. Shaidun ganin ido sun ce matasan sun yi kama da 'yan asalin arewacin Afirka, to sai dai har ya zuwa yanzu ba a tabbatar da asalin kasashen da suka fito ba.

Abin da ke a fili shi ne dukkansu sun bugu kuma sun yi ta jifa da kayan wasan wuta cikin jama'a, inji 'yan sanda. Sai da misali karfe daya na dare 'yan sanda suka samu takamammen labari na cin zarafi. Tambayar da ake ita ce mai ya sa irin wannan abu zai faru a wuri mai muhimmanci kuma a wannan dare na bikin shiga sabuwar shekara? Mai yasa lamarin ya fi karfin 'yan sanda?

Ibrahim Öztürk mai kantin sayar da gwala-gwalai ne a daura da tashar ya zargi 'yan sanda ne da gazawa.

"Ba mu jin tsoron cewa wani abu zai iya faruwa a nan. Amma ma'aikatanmu muke tsoro ka da wani abu ya rutsa da su. Mata da yawa na aiki a nan, kuma muna bude kanti da dare. Akwai 'yan sanda 200 lokacin amma sun kasa shawo kan lamarin. Wadannan fa jami'ai ne da suka samu horon tinkarar irin wannan lamari. Ai ba a bukatar 'yan sanda dubu daya don sa ido kan mutane dubu daya. Ni 'yan sanda ne dora wa laifi."

Yanzu haka mahukuntan birnin Kolon na kokarin kwantar da hankalin jama'a, suka ce za su kara yawan 'yan sanda ana kuma tattaunawa kan kara yawan kyamarorin bidiyo a cikin tashar.